Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home ยป Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran
SPORT:::::::::::::

Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami'an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran

iGeekBy iGeekMay 9, 2017No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Tsananin Kama Da Messi Ta Sa Jami’an Tsaro Kama Wani Dalibi A Kasar Iran

A karshen mako ne, aka samu wani rudani wanda har sai da ‘yan sanda suka dauke wani dalibi dan kasar Iran suka kai shi ofishinsu saboda yana matukar kama da Lionel Messi

Mutane da yawa a birnin Hamaden na kasar ta Iran suna son daukar hoto da dalibin mai suna Reza Parastesh yayin da ‘yan sanda suka kama motarsa domin dakatar da rudanin da hakan ya haddasa.

Lamarin ya faru ne, watanni kadan bayan da mahaifin Reza Parastesh ya sa dan nasa ya dauki hoto da rigar Barcelona mai lamba 10 irin ta Messi.

Daga nan sai matashin mai shekara 25 ya fara yin aski tare da barin gemunsa kamar yadda Messi yake yi.

Hakkin mallakar hotoGetty Images
Image caption Ana rokon Parastesh yin hotuna a birnin Hameden, na kasar Iran
Ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “Yanzu mutane suna daukarsa a matsayin Messi na Iran, kuma suna so in rika kwaikwayon duk abin da yake yi. Idan na je wani wurin sai ka ga mutane suna matukar mamaki.

” Ina matukar murna ganin cewa ganina zai sanya wasu farin ciki, kuma wannan farin ciki yakan sa ni farin ciki sosai.”

Ya kuma ce yana koyon yadda ake wasu abubuwan a wasan kwallon kafa ta yadda zai zama kamar Messin sosai.

Rahoton BBC

Advertisements

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Sevilla Ta Karya Tarihin Shekara (60) Na Manchester United

March 16, 2018

Real Madrid Sun Shiga Sahun Mahaukata Akan De Gea – Mourinho

March 16, 2018

Ina So Allah Ya Hadamu Da Liverpool ko Real Madrid – Dzeko

March 16, 2018
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.