Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home » 'Ku daina yadda da jita-jitar mutuwar Shugaba Buhari' -inyi Mai magana da yawunsa mal Garba shehu
NEWS

'Ku daina yadda da jita-jitar mutuwar Shugaba Buhari' -inyi Mai magana da yawunsa mal Garba shehu

iGeekBy iGeekMay 15, 2017No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email


Fadar shugaban kasar Najeriya ta yi Allah-wadai da sabuwar jita-jitar da ake yaɗawa kan mutuwar Shugaba Muhammadu Buhari, tana mai bayyana hakan da cewa wata manaƙisa ce kawai da ake shiryawa don sanya fargaba a zuƙatan ‘yan ƙasar.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ne ya yi wannan kira a shafinsa na Twitter.
Ya kuma sake kira ga ‘yan Najeriyar cewa, duk wanda ya samu wani bayani a Whatsapp ko Facebook, to kada ya yarda da batun don kuwa ‘ƙarya ce tsagwaronta’ aka yi wa al’umma don sanya musu fargaba.
Malam Garba Shehu ya rubuta cewa, 

“Ana ta yada jita-jita marar madogara a shafukan sada zumunta cewa wani abu marar daɗi ya faru ga shugaban kasarmu abin kaunarmu Muhammadu Buhari.
“Ba wani abu da ya sami shugaban kasa. Babu wani dalili na damuwa. Mun gode da kiran wayoyin da muka samu.”

Shi ma a nasa bangaren, babban mai bai wa shugaba Buharin shawara kan harkar yada labari, Femi Adesina, ya rubuta a shafin nasa na Twitter cewa, “Me ya sa wasu mutanen suke muguwar fata da mugun tunani? Sai abin da Allah ya so ne kawai zai faru. Allah ya albarkaci duk masu yi wa Shugaba Buhari addu’ar alheri.”

A watan Janairu ma lokacin da Shugaba Buhari ya tafi birnin London din, an yi ta yaɗa jita-jita a Najeriya cewa ya mutu.

Shugaba Buhari ya tafi Ingila ne a ranar 7 ga watan Mayun nan, don sake ganin likita a kan rashin lafiyar da yake fama da ita, sai dai fadar shugaban ta ce likitoci ne za su fadi ranar da zai kammala ya dawo.
Sai dai kafin tafiyar tasa ya shafe tsawon mako biyu bai fito taro jama’a ba, al’amarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kasar, inda har wasu kungiyoyi suka dinga kiransa da ya koma ganin likita, yayin da wasu kuwa suke cewa ya yi murabus in ba zai iya ba.

Rahoto:bbchausa

Advertisements

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

President Buhari Signs Proclamation Proscribing IPOB

September 19, 2017

Full Text Of President Buhari’s Address At The 72nd United Nations General Assembly | READ

September 19, 2017

BREAKING NEWS:- Two Suicide Bombers Storm Borno, 15 People Killed

September 18, 2017
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.