Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home » Dalilinda Yasa Na Shigo Harka Fim Inji Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya
kannywood

Dalilinda Yasa Na Shigo Harka Fim Inji Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya

iGeekBy iGeekJuly 28, 2017No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood, Aisha Aliyu, wacce aka fi sani da suna Aisha Tsamiya ta shaida wa BBC cewa babu fim din da ya taba ba ta wahala kamar “Dakin Amarya”.

Fim din Dakin Amarya yana magana ne kan yadda mata ke bakin kishi, musamman idan aka auro musu abokiyar zama – ta fito ne a matsayin kishiyar Halima Atete, wacce ita ce uwar gidan Ali Nuhu.

“Sai da na ji rauni na gaske a fim din musamman saboda yadda aka rika yin fatali da kayan daki irinsu tangaran da talabijin”, in ji Aisha Tsamiya, a hirar da ta yi da .
Jarumar ta kara da cewa tun tana karama take sha’awar fitowa a fina-finan Kannywood “saboda suna matukar burge ni”.

A cewarta, “Na dauki yin fim a matsayin sana’a don haka ina jin dadin fitowa a cikinsa.”
Tsamiya, wacce ta soma fim a shekarar 2011, ta kara da cewa dukkan jaruman da ke yin fim tare da ita suna burge ta “kuma ina zaune da kowannensu lafiya”.
“Jarumai irinsu su Adamu (Adam A. Zango), Sadiq Sani Sadiq, Zahraddeen Sani, da dukkansu sauran jarumai suna burge ni. Haka ma mata jarumai, dukkansu ina zaune da su lafiya kuma suna burge ni”, in ji Aisha Aliyu.

Ta ce ta soma fitowa a fim din Tsamiya ne shi ya sa aka sanya mata wannan suna.
Aisha dai ta fi fitowa a fina-finan da ke nuna ta a mutuniyar kirki, wacce kuma ake tauyewa hakki.

Advertisements

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Yadda wasu fitattun jaruman sunka kwashe shekaru cikin masana’atar fim

January 30, 2023

Hirar murya kunya yar tiktok a hannun yan sanda

January 30, 2023

Karshen Tika Tik : Lilin Baba Ya Bayyana Hotunan Yaronsa Na Farko

January 10, 2023
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.