An dakatar da Ronaldo buga wasa biyar
-
Mintuna 28 da suka wuce
- Aika
Advertisements

An dakatar da Cristiano Ronaldo daga buga wasa biyar, bayan da aka ba shi jan kati a karawar da Real Madrid ta ci Barcelona 3-1 a Spanish Super Cup a ranar Lahadi.
An dakatar da Ronaldo wasa daya, bayan da aka ba shi katin gargadi biyu a Nou Camp, daya saboda ya cire rigarsa bayan da ya ci kwallo na biyu kuma ya fadi a da’ira ta 18 ta Barcelona da gangan.
An kara mai hukuncin wasa hudu saboda ya ture alkalin wasa, bayan da ya ba shi jan katin.
Ronaldo ba zai buga wasa na biyu da Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona ba.
sources:bbchausa.com