Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta yi kaca-kaca da wasu limamai masu annabta ƙarya, bayan wankin hula da annabin Afirka ta Kudu, Joshua Mhlakela, wanda ya yi ikirarin cewa “rapture” zai faru a ranar 23 zuwa 24 ga Satumba.
Advertisements
Mhlakela ya bayyana cewa Yesu Kristi ya bayyana masa a mafarki tare da ba shi kwanan wata na dawowar Ubangiji. Ya ce rapture zai zo daidai lokacin bikin Yahudawa na Feast of Trumpets (Rosh Hashanah). Wannan annabci nasa ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta, musamman TikTok da YouTube, inda dubban mabiyansa suka ɗauki matakai masu tsanani.
Rayuka Sun Taba Da Rawa
Wasu mabiya sun yi murabus daga aikinsu, sun sayar da gidaje da motoci, wasu kuma sun raba kayansu kyauta saboda suna ganin ba za su sake amfani da su a duniya ba. Hashtag ɗin #RaptureTok ya cika da shirye-shiryen mutane da suka yi imani cewa ƙarshen duniya ya zo.
Wata mace ta koka cewa ta bar aikinta da dukiyarta, amma ta wayi gari duniya tana nan daram. Wani saurayi kuma ya bayyana cewa ya ji kansa kamar wawa, saboda ya raba dukiyarsa ya rasa komai, yanzu kuma yana shakku a bangaskiyarsa.
Bidiyoyi sun nuna tarin mutane a daji suna jiran a ɗauke su, yayin da Mhlakela kansa ya shiga live yana cewa rapture yana kusa. Amma bayan sa’o’i sun ja babu abin da ya faru, sai fargaba ta rikide ta zama takaici da kuka.
Shugabannin Addini Sun Mayar Da Martani
Fasto Chris Okotie daga Najeriya ya yi watsi da annabcin Mhlakela, inda ya bayyana shi a matsayin “shirme na limamin ƙarya.” Ya ce wannan koyarwar ta saba da Linjila, kuma bai kamata Kirista ya ɗaura bangaskiya da tsayayyen kwanan wata ba.
Haka nan, Daraktan Harkokin Jama’a na CAN, Abimbola Ayuba, ya caccaki irin waɗannan limaman masu ruɗi. Ya bukaci gwamnati ta ɗauki matakin hukunta su, inda ma ya yi tsokaci cewa: “Wannan faston da ya yi ƙarya ya fi dacewa a ‘rapture’ cikin gidan yari.”
Tarihin Annabcin Ƙarya
Ko da yake rapture ra’ayi ne da ake yarda da shi a Kiristanci, tarihi ya nuna cewa yawancin annabawan da suka taɓa faɗin kwanan wata sun sha karya. Malaman addini sun gargadi jama’a da cewa irin wannan tsinkaye ba wai kawai ya lalata imani ba ne, har ma yana rusa rayuwar masu bin sa.
A ƙarshe, wannan ƙaryar rapture ta Satumba ta zama darasi ga mabiya cewa kada su jingina bangaskiyarsu da kalaman malamai marasa tushe, domin kada su sake shiga cikin ruɗin da zai hallaka rayuwarsu.
