Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Home » Sirrin da ke tattare da cin danyen Tumatir musamman ga mai Azumi
    NEWS

    Sirrin da ke tattare da cin danyen Tumatir musamman ga mai Azumi

    iGeekBy iGeekMay 31, 2017No Comments2 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

    Sirrin da ke tattare da cin danyen Tumatir musamman ga mai Azumi
    Wani dalibi a jami’ar Maiduguri mai suna Jesse Tafida ya binciko wadansu hanyoyi da za a iya amfani da danyen tumatir wajen karfafa garkuwar jika da samar wa jiki lafiyar da take bukata, da kuma amfanin da ke gareshi a jikin dan Adam musamman yanzu da musulmai ke azumin watan Ramadan.
    Ya ce ya gano hakan ne bayan binciken da ya gudanar akan sinadarorin da dayen tumatir ke dauke da su da mutane da yawa basu sani ba.
    Tafida ya gano cewa tumatir na dauke da sunadarin da ake kira ‘Antioxidants’ a turance da ke kare mutum daga kamuwa daga wasu cututtuka sannan kuma ana samun sinadarin Vitamins A da B da kuma Folic Acid a cikinsa.
    Dalibin yace cin dayen tumatir na kare mutum daga kamuwa da cutar daji, hawan jini da kuma bugawar zuciya.
    Ya ce wasu binciken sun nuna cewa idan ana gauraya danyen tumatir a cikin abinci musamman cikin wasu gaiyayyakin da ake ci kamar zogale, rama da makamatansu yana rage cutar siga.
    Ya kuma ce za a iya cin dayen tumatir idan cikin mutum ya murde ko kuma idan cikin mutum na ciwo sannan yana kuma rage kiba a jiki musamman ga wadanda suke bukatar haka.
    Tafida ya ce cin dayen tumatir na kara karfin ido da kuma ya kare idon daga kamuwa daga wasu cututtuka kamar yanar ido, amosanin ido da makamatan su.
    Daga karshe ya shawarci matan da suke dauke da juna biyu da su yawaita cin dayen tumatir lokacin da suke da ciki da kuma bayan sun haihu domin yana taimakawa wajen kare jariri daga kamuwa da cututtuka da kuma taimaka masa wajen girma.

    Rahoto:premium hausa times

    Advertisements

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    iGeek
    • Website

    Related Posts

    Mai Boutique Ya Fitar da Wraps 127 na Kwayar Cocaine Bayan Komowa Daga Thailand

    October 13, 2025

    Mahmood Yakubu Ya Gane Fasaha Ta Inganta Zabe Amma Ba Za Ta Iya Kawar Da Matsalolin Siyasa Ba

    October 13, 2025

    Kungiyar Malaman Kudu ta Kaduna Ta Nemi Sanata Katung Ya Bar PDP, Ya Shiga APC Don Ci Gaban Yankin

    October 13, 2025
    Leave A Reply Cancel Reply

    Recent Comments
    • Nasiru sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • Nasiri sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
    • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
    • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
    © 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.