Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Home ยป Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al'umma – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo
    FATAWA

    Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al'umma – Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

    iGeekBy iGeekFebruary 14, 2017No Comments1 Min Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

    Wajibi Ne Shugaba Ya Nisanci Dukiyar Al’umma:

    Wajibi ne shugaba ya zama mai kamewa daga taba dukiyar al’ummarsa.kada ya zama mai kwadayi akanta.Idan yana da wadatar dukiya ya yi musu aiki ba tare da ya karbi haraji daga hannunsa ba.Yin hakan yana daga cikar adalci da karamci da shugaba na kwarai zai nuna .Ka dubu Zul-karnaini yayin da jama’a suka yi masa tayin su biya shi lada,don ya yi musu ganuwa tsakanin Yajuju da Majuju ,masu shigowa gari suna musu barna da ta’addanci. Sai ya nuna musu cewa,abin da Allah ya hore mishi ya ishe shi,ba sai ya karbi na hannunsu ba.

    Don haka ya yi musu katanga mai karfi ta kare da narkakkiyar dalma,ba tare da sun biya ko kwabo ba,in banda ma’aikata da wasu kayan aiki da ya nema daga wajensu.Allah ya bamu labarin hakan inda yace ,(“suka ce,”Ya Zul-karnaini! lallai Yajuju da Majuju masu barna ne a bayan kasa,shin mu baka wani lada ka gina ganuwa tsakaninmu da su.”sai yace ,”Abin da ubangijina ya ba ni ya fi mini Alheri ,amma ku taimaka min da karfi don in sanya muku ganuwa ta kankare tsakaninku da su.”[Al-kahfi,94-95]

    Advertisements

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    iGeek
    • Website

    Related Posts

    Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

    March 12, 2018

    Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

    February 18, 2018

    [Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto

    July 24, 2017
    Leave A Reply Cancel Reply

    Recent Comments
    • Nasiru sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • Nasiri sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
    • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
    • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
    © 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.