Abuja, babban birnin tarayya, na fama da wata sabuwar matsala da ta zama abin damuwa ga iyaye da ƙwararru. A yawancin unguwannin da ke wajen gari (satellite towns), ana kafa makarantu ƙananan da ba su da inganci, wadanda suka fi kama da wuraren kasuwanci fiye da cibiyoyin koyarwa.
Advertisements
Masu ruwa da tsaki sun yi gargadin cewa yawaitar irin waɗannan makarantu, tare da sakacin hukumomin kula da ilimi, na iya jefa tsarin ilimi cikin mummunar tabarbarewa.
Ilimi: Daga Hakki Zuwa Sana’a
A tarihi, ilimi ana ɗaukarsa a matsayin hakkin ɗan ƙasa da kuma babbar hanya ta samun cigaba. Manyan jagororin Najeriya irin su Chief Obafemi Awolowo sun yi amfani da ilimi wajen wayar da kan al’umma da kuma samar da cigaba.
Amma lalacewar makarantun gwamnati ya sa iyaye da dama suka koma ga na kashin kansu. A yau, ilimi ya koma wata hanya ta kasuwanci. Duk wanda ke da ƙaramin kuɗi zai iya buɗe makaranta, ko da bai da ƙwarewa
Makarantu Marasa Inganci a Unguwannin Abuja
Bincike ya nuna cewa makarantu a unguwannin Kurudu, Kpeyegi da Orozo suna fama da matsaloli iri ɗaya: babu ɗakunan karatu, babu dakin gwaje-gwaje, babu filayen wasanni, kuma malamai ba su da ƙwarewa. Duk da haka, iyaye na biyan kuɗi mai tsada, alhali malaman suna karɓar kuɗin aljihun talaka.
A Kurudu, wani gida mai ɗakuna uku ya koma aji. Wata matashiya mara kwarewar koyarwa ce ke koyar da yara goma ba tare da tsarin kundin karatu ba. Lokacin da aka tambaye ta, sai ta ce:
“Ina koya musu abubuwan da nake ganin ya kamata su sani. Ba mu da curriculum yanzu. Soyayyar koyarwa ce kawai ta sa na fara.”
Lifespring Academy: Tana da Rajista, Amma Babu Kayan Aiki
A Lifespring Academy da ke Kurudu, an fi samun tsari. Makarantar na da rajistar WAEC da NECO, amma tana fama da matsalar rashin malamai masu kwarewa da wuraren wasanni. Dalibai na amfani da filayen makarantar gwamnati don gudanar da taron wasanni.
Wani mazaunin wurin, Mr. Joshua, ya bayyana damuwarsa:
“Komai ya koma kasuwanci. Amma bai kamata mu yi wasa da ilimi da lafiya ba. Idan aka yi wasa da su, gaba ɗaya rayuwa ta lalace.”
Ivy Academy da Graceland International: Kyalli Na Waje Kawai
A Ivy Academy, Kpeyegi, akwai wasu malamai masu takardar shaidar sakandare kawai, suna koyar da yara. A Graceland International, Orozo, babban gini mai kayatarwa yana nuna kamar komai yana tafiya daidai, amma a ciki akwai matsalolin malamai da tsarin ilimi mara tsari.
Makomar Ilimin Abuja a Hadari
Masana sun yi gargadin cewa barin irin waɗannan makarantu na ci gaba da aiki ba tare da kulawa ba na iya lalata makomar yara. A yayin da hukumomi ke kauda kai, yara na samun ilimi mara inganci wanda ba zai iya taimaka musu a gaba ba.
Iyaye masu ƙaramin karfi na ganin waɗannan makarantu a matsayin mafita mai sauƙi, amma farashin da za a biya daga baya na iya zama mafi tsada ga makomar Najeriya.
