Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Hausaloaded
    Home ยป ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?
    FATAWA

    ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?

    iGeekBy iGeekAugust 14, 2016No Comments1 Min Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

    ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA ?

    Advertisements

    Tambaya

    Asalamu Alaikum.
    Allah ya karawa Dr Fikira da Fasaha.

    Tambaya: idan mutum yazo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta S Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa dashi suna ji?

    Amsa

    Wa alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake  hudubar juma’a bai game har da pre khudba ba,don haka za ka iya yin magana,ko ka karanta alqur’ani a lokacin da ake yinta.                                      

    Pre- khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma’a ya shiga,sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari’a abu ne da yake hanun Allah da manzonsa, wannan ya sa za’a takaita a inda ya zo a nan.                                                    
    Hadisi mai lamba ta: 841 a sahihil Bukhari ya tabbatar da cewa : sai liman ya fito zai hau minbari ya fara huduba sannan mala’iku suke nannade takardun su,su zauna su saurari wa’azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma’a wajan wajabta yin shiru da sauraro.                                                                                                            
    Allah ne mafi sani.

    Dr Jamilu Zarewa.                   3/Ramadan 1437

    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
    iGeek
    • Website

    Related Posts

    Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

    March 12, 2018

    Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

    February 18, 2018

    [Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto

    July 24, 2017
    Leave A Reply Cancel Reply

    Recent Comments
    • Nasiru sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • Nasiri sambo on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
    • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
    • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
    Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
    © 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.